Tuesday, March 10
Shadow

Labaran Soyayya Masu Dadi da koyar da darasin Rayuwa

Sannun ku da zuwa blog dinmu a daidai wannan lokacin, barkan mu da kasancewa tare a daidai wannan lokacin, A wannan zamanin da muke ciki, soyayya tana da matukar muhimmanci ga kowa. Wasu lokuta, labaran soyayya kamar a fina-finai, suna bayyana abubuwa masu kyau da ban mamaki. Wannan shine labarin soyayya na Amina da Usman, wanda ya faru a wannan kasar tamu

Amina dai tana karatun digiri a makarantar koyon kimiyya, yayin da Usman yake aiki a wani shahararren kamfani a garin. sun hadu ne a yayi wani taron wayar dakai, inda Amina ta yi jawabi kan muhimmancin ilimi ga mata. Usman ya kasance cikin masu sauraron ta, a lokacin da ta fara Bada jawabi, zuciyarsa ta Riga ta kaimu da santa.

Bayan taron, Usman ya yi shirin yin magana da Amina. Ya yi tunanin yadda zai bayyana aniyarsa gare ta. A lokacin da suka fara tattaunawa, sun fahimci cewa suna da kaman ceceniya a Cikin al’amuran su. Suna sha’awar karatu, Wasan motsa jiki da kuma yin tafiya.

Bayan makonni biyu da wannan taron, Usman ya yanke shawarar kiran Amina don fita tare. Ya zabi wani shahararren wurin cin abunci a cikin garin. Inda suka siya kallan abuncin da suke so, suna ci suna hiran su irin na Masoya.

“Na ji dadin lokacin da muke tare, Amina,” in ji Usman, yana kallon idanunta. “Kina da guri na musamman a zuciyata.”

Amina ta yi murmushi, zuciyarta cika da farin ciki. “Ni ma haka nake ji, Usman. Ina ji cewa haduwan mu Alkhairi ne.”

Bayan wannan rana, Masoyan gida biyu sun kulla alakar soyayya mai karfi. Sun kasance masu ziyartar wurare masu kyau a cikin garin, suna tattaunawa akan burinsu na rayuwa. Amina ta raba burinta na zama likita, yayin da Usman ya bayyana sha’awarsa na zama mai gudanarwa a kamfanin da yake aiki. Sun yi alkawarin goyon bayan juna a kowane mataki na Rayuwa

A sanin mutane, kyauta tana Kara karfin Soyayya, abokantaka da Kuma zamantakewa, Usman ma ya San da haka shiyasa ya yanke shawarar kawo wa Amina kyaututtuka na musamman. yana kawo mata ƙaramin kyauta, ko da kuwa kayan marmari ne ko wani abu na musamman. Amina tana farin ciki da wannan kyautar, zuciyar ta, ta yarda cewa Usman yana tunawa da ita a kowane lokaci.

Bayan wasu Lokaci  yan kadan da aka kwashe suna soyayya, Masoyan biyu sun yanke shawarar zama tare har abada. Sun yi aure kuma an shaida inda dangi da abokai suka taru don murnar wannan biki mai Albarka. Labarinsu ya zama abin koyi ga wasu, yana nuna cewa soyayya tana da karfi da kuma kyawawan abubuwa.

A karshe, Amina da Usman sun koyi darasi mai mahimmanci: soyayya tana bukatar hakuri, goyon baya, da kuma jituwa. Wannan labarin soyayya na su ya kasance mai dadi, yana tunatar da mu cewa a duniya, akwai kyawawan labarai da ke nuna Soyayya na gaskiya. Allah ya datar damu akan soyayyar mu da auren mu Ameen